<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>6</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Mu yi sujada ga Ubangiji,
 Mu yi godiya domin ƙaunarsa.
 Da zuciya ɗaya mu ɗaukaka shi,
 Mu yabi sunansa da duk ladabi.

[V2]
 2) Mu yi tunani a kan girmansa,
 Mu yi waƙoƙi kan alherinsa,
 Mai Tsarki, Mai Ƙauna, Mai Gaskiya ne,
 Mai ikon halitta, mai jin addu'a.

[V3]
 3) Bukatarmu duk shi ya ke ta biya,
 Mu karƃe su fa tare da godiya.
 Abinci, abin sha, numfashi da rai,
 Lissafin kyautansa ya fi ƙarfinmu.

[V4]
 4) Mu raunana ne, amma cetattu,
 Mu ƴaƴansa ne, bai yashe mu ba.
 Yana marmari dai mu yi zumunta,
 Jiƙansa mai yawa, ba misalinsa.

[V5]
 5) Al'amuranmu su girmama shi,
 Da bakunanmu mu yi ta shaida.
 Mu bauta masa, mu ji tsoronsa kuwa,
 Gama shi ne Allah na duk duniya.</lyrics>
<title>Mu Yi Sujada Ga Ubangiji LW6</title>
</song>